Martani Ga Arewa: Yarbawa Za Su Fara Yajin Aikin Cin Nama

Kungiyar kare hakkin Yarbawa ta Afenifere, tare da sanannen ɗan ta’addan nan Gani Adams, Sunday Adeyemo wanda akewa lakabi da Igboho da kuma Mutanen Odua karkashin jagorancin yarima Segun Osinbote sun shirya tsaf domin kaddamar da shirin nuna kyamar amfani da naman shanu a yankin.

Shirin wanda suka yiwa lakabi da “Anything, But Cow Day” za’a kaddamar dashi a ranar Jumua, 5 ga watan Maris din da muke ciki 2020.

An shirya hakan ne biyo bayan kauracewar da ‘yan kasuwar arewa sukayi wa kudancin kasar na kai kayayyakin amfanin gona da dabbobi kimanin kwanaki biyar.

A halin yanzu dai, Yajin aikin da masu dillancin shanu da kayan abinci suka fara karkashin hadakar kungiyoyin masu dillancin Shanu da kayan abinci na kasa (AUFCDN) ya shiga kwana na 5 Yajin aikin wanda ya kunshi kulle duk wata hanyar da za’a iya kai kaya data hada Arewacin kasar da Kudanci.

A wani taro da tayi ranar Litinin a Abuja, Ƙungiyar dillalan kayayyakin abinci na Arewa AUFCDN tace, an gayyaci shugabannin ta zuwa hukumar DSS akan hana safarar kayan abinci da kuma shanu daga arewaci zuwa kudancin kasar.

Sakataren AUFCDN , Ahmed Alaramma, ya kara da cewa a yanzu haka shugaban kungiyar na tare da Jami’an tsaro na farin kaya DSS.

Labarai Makamanta