Manyan ‘Yan Kasuwa Da ‘Yan Siyasa Sun Yi Taron Ceto Najeriya A Legas

Rahotannin dake shigo mana daga Ikko babban birnin Jihar Legas na bayyana cewa manyan mutane kimanin 100 da su ka kunshi ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa masana da kwararru sun yi wani taro a Legas domin fito da yadda za a ceci Najeriya.

An ruwaito cewa taron ya hada da gwamnoni 14 masu-ci da tsofaffin gwamnonin jihohi 13 da wasu shugabannin majalisar dattawa uku da aka taba yi. Wadannan jagorori a karkashin inuwar ‘The 2022 Committee’ sun ce ya zama dole a samar da zaman lafiya a kasa kafin a fara yin maganar takara a 2023.

‘Yan kwamitin na ‘The 2022 Committee’ sun fitar da jawabin bayan taro ne ta bakin shugabanninsu; Nduka Obaigbena da Kashim Ibrahim-Imam. Obaigbena da Ibrahim-Imam sun bayyana cewa kwamitin na su ya yi aiki a kan tattalin arziki, tsaro da shirin mika mulki domin ganin halin da ake ciki a yau.

Kwamitin ya yi kira ga duk masu kishin-kasa da suke sha’awar a kawo gyara a Najeriya, su shigo cikinsu domin ganin an samu kasar da za ayi alfahari da ita anan gaba.

Kwamitin ya sanar da jama’a cewa bai da nufin yi wa wani ‘dan takara ko jam’iyyar siyasa aiki.

Labarai Makamanta