Manyan Mutane Ke Daukar Nauyin ‘Yan Ta’adda A Neja – Gwamnan Neja

Gwamnan jahar Neja, Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa akwai wasu manyan mutane a jahar dake baiwa yan bindiga, barayin shanu da masu garkuwa da mutane bayanan sirri.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito kimanin kananan hukumomi 5 yan bindiga suka addaba da suka hada da Rafi, Shiroro, Mariga, Lapai da kuma Munya.

‘Yan bindigan sun kashe jama’a, sun sace na sacewa sa’annan sun lalata dimbin dukiyoyi na miliyoyin nairori, tare da sabbaba dubunnan mutane yin gudun hijira.

Kakakin gwamnan, Mary Noel-Berje ce ta sanar da haka a ranar Alhamis, inda tace wannan zagon kasan shi ne abin da yasa hukumomin tsaro basu samun galaba a kan miyagun.

“Wannan ba karamin matsala bane, saboda yan bindigan suna aiki ne tare da wasu manyan mutane a garuruwan da ake kai harin, su ke basu bayanan sirri, da haka suke tsallake tarko da jami’an tsaro ke sanya musu.” Inji ta.

Don haka gwamnan ya nemi jama’a su taimaka ma gwamnati a yakin da take yi da miyagun yan bindiga ta hanyar kai rahoton duk wanda suka sani yana aiki da yan bindigan.

Haka zalika gwamnan ya bayyana girman fadin kasar jahar da girman dazukanta a matsayin wani kalubale da hukumomin tsaro suke fuskanta, saboda a dazukan yan bindiga suke fakewa.

“Ina tabbatar muku da cewa muna iya kokarinmu don tabbatar da mun samar da ingantacce tsaro ga jama’anmu, zamu nasara ne a kan miyagu idan muna samun bayanan sirri game da ayyukansu, don haka muke bukatar taimakon kowa.” Inji shi.

Related posts