Manyan Hafsoshin Tsaro Sun Jaddada Mubaya’a Ga Buhari

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Manyan hafsoshin tsaro sun sake yin alkawarin biyayya ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tare da karyata duk wani shiri na kifar da gwamnatin.

Wannan tabbacin ya fito ne daga bakin hafsoshin sojan yayin ganawa da manema labarai tare da manyan editocin manyan kungiyoyin yada labarai na gargajiya da na yanar gizo a Najeriya.

“Rundunar Sojoji ta nisanta kanta daga irin wadannan kiraye-kirayen,” in ji Shugaban ma’aikatan Tsaro, Janar Lucky Irabor. Tattaunawar wacce aka yiwa lakabi da Tattaunawar Bude Kunnen Jarida ta kuma samu halartar Shugaban Ma’aikatan Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo da wakilin Babban Hafsan Sojan Sama Oladayo Amao.

Shugaban hafsan sojin kasa Ibrahim Attahiru bai halarci taron ba. Janar Irabor, tsohon kwamandan atisayen Operation Lafiya Dole, ya bayyana cewa jawabin ya kasance ne domin jin ra’ayoyin jama’a game da ayyukan sojoji a kokarin kare kasar a cikin kwanaki 100 da suka gabata na kasancewa kan mulki da kuma yadda za a inganta ci gaba.

Shima da yake jawabi a wajen taron, Shugaban hafsan sojojin ruwa, Vice Admiral Gambo ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa sojoji na matukar kokarin shawo kan matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a kasar wanda kuma ya shafi ma’aikatan soji.

Ya bayyana cewa daya daga cikin dabarun da sojoji za su dauka don dakile kwararar makamai wanda ke kara tabarbarewar tsaro a Najeriya shi ne mayar da rundunar sojan ruwa zuwa tashar jiragen ruwa.

“Sojojin ruwa na son komawa tashar jiragen ruwa inda muka kasance ba mu nan kusan shekaru 3. A duk faɗin duniya, ƙa’ida ce a samu tashar sojin ruwa a tashoshin jiragen ruwa,” in ji Gambo.

Da kasancewar sojojin ruwa, Vice Admiral Gambo yana da kwarin gwiwar cewa za a dakile shigo da makamai cikin kasar ta tashoshin ruwan teku don haifar da rashin tsaro. Game da tayar da kayar baya da ta’addanci a arewa, ya bayyana cewa sojoji suna aiki kan wani tanadi don shirya ‘yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya da za su karbe iko da kuma rike filayen da sojoji suka ci nasara.

Vice Admiral Gambo ya lura cewa shugabannin hafsoshin sun fi yin aiki sosai kuma ba su cika magana ba amma yanzu suna bukatar jin karfin al’umma game da sakamakon su cikin kwanaki 100 da suka gabata.

“Mun kasance muna daukar matakai, bamu cika magana ba dangane da umarnin shugaban kasa da shugaban ma’aikatan tsaro.” Air Marshall Amao ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya ta bakin wakilin sa cewa sojoji, musamman rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF), na samun kayan aikin da suka dace don magance ta’addanci da‘ yan fashi.

“Muna karbar sako irin na jiragen JF17 Thunder, UAVs na musamman da Super Tucanos. Air Marshall Amao yana nanata shirye-shiryen tarbar Tucanos,” ya bayyana.

Game da jirgin yakin NAF Alpha da ya fadi a dajin Sambisa, Amao ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin, kuma ba zai kyautu ba a fitar da sanarwa a hukumance wanda daga baya za a janye shi.

Labarai Makamanta