Manchester City Ta Musanta Daukar Messi

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta fito fili inda ta nesanta kanta daga batun daukar dan wasan Barcelona Lionel Messi.

Batun yiwuwar fitar da Barcelona daga gasar Zakarun Turai da wuri ya haifar da rade-radin cewa Messi zai iya barin Nou Camp.

An fada cikin halin rashin tabbas game da makomar dan wasan, yayin da dukkan masu takarar shugabancin Barcelona suka jaddada aniyarsu ta ganin dan wasan mai shekara 33 ya ci gaba da zama a kungiyar.

Messi ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta Ballon D’Or sau shida a tarihin tamaularsa inda ake yi masa kallo a matsayin daya daga cikin fitattun ‘yan kwallon da ba a taba yin irin su ba.

City ta dade tana duba yiwuwar daukar dan wasan, musamman ganin alakarsa da tsohon kocin Barcelona Pep Guardiola, kodayake an ce Paris St-Germain ma tana son daukar dan wasan.

Rahotanni sun ce City ta gabatar da kwantaragin da za ta bai wa Messi wanda ta yi wa kwaskwarima amma wata majiya a kungiyar ta shaida wa BBC Sport cewa hakan ba gaskiya ba ne – kuma ba a taba yi masa wani tayi ba, a lokacin bazara, ko kuma kafin hakan, sannan ba a wata tattaunawa kan batun a halin da ake ciki.

Messi ya shirya tsaf domin tafiya City har ma a watan Agusta ya nemi raba aurensa da Barcelona amma tsohon shugaban kungiyar Josep Maria Bartomeu ya hana shi tafiya kodayake ya ajiye aiki a watan Oktoba.

Labarai Makamanta