Malaman Addini Sun Taimaka Wajen Sake Dawowar CORONA – Gwamnatin Tarayya

Kwamitin Fadar Shugaban ƙasa mai yaki da annobar COVID-19 a Najeriya PTF ya zargi wasu kungiyoyin addini da saba dokoki da sharudodin da aka gindaya a kasar, wanda hakan ya taimaka wajen sake dawowar cutar CORONA ɗanya sharaf a Najeriya.

Kwamitin ya yi wannan magana ne bayan an fara samun karuwar masu dauke da cutar a cikin ‘yan kwanakin nan, inda lamarin ya yi kamari sosai a Jihohi da dama a Najeriya.

Da yake jawabi a ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba, 2020, Shugaban kwamitin kuma Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya zargi malamai da Pastoci wajen yin ƙafar ungulu akan ƙoƙarin gwamnati na kawar da cutar a Najeriya.

Mista Boss Mustapha ya ƙara da cewa kungiyoyin addini sun rika kawo cikas ta hanyar tara jama’a da sunan tarukan addini ba tare da la’akari da ka’idoji ba.

Mustapha ya yi wa manema labarai bayanin yadda annobar ta yi tasiri a al’umma ta hanyar jawo rikici, tabarbarewar lafiyar kwakwalwa da shan kwayoyi. Shugaban yaƙi da CORONAN yace kwamitin na aiki da masu fada a ji da masu ruwa da tsaki domin ganin an shawo kan wadanna matsaloli da ake fuskanta dalilin annobar.

“Mun lura cewa, abin takaici ne yadda ‘yan Najeriya, musamman kungiyoyin addini, suka cigaba da shirya manyan taruka da ke iya yada cutar ba tare da nuna wata kulawa ba.

“Muna kira ga duk kungiyoyin kasa cewa babban nauyi ne a kansu su tabbatar an bi doka da sharudan da aka gindaya domin hana yaduwar cutar.” Inji Mustapha.

Labarai Makamanta

Leave a Reply