Malaman Addini Sun Fi ‘Yan Siyasa Lalata – Aisha Yesufu

Shahararriyar ‘yar fafutukan nan, Aisha Yesufu, ta bayyana cewa shugabannin addinai suna amfana daga shugabanci mara kyau, wanda hakan ya taimaka musu na shiga rudu da lalacewar da ta fi ‘yan siyasa.

Aisha Yesufu ta faɗi haka ne yayin da take martani kan maganar da shugaban Deeper Christian Life Ministry, William Kumuyi, wanda ya gargaɗi kiristoci su daina zagin shugabanni.

William Kumuyi ya yi magana kan rashin kyaun shiga duk wani abu da zai jawo lalata kayayyaki da dukiyoyin mutane da na gwamnati saboda gaza cika alƙawarurran yan siyasa.

Faston yace: “Mun koyar daku matukar kana da cikakken imanin kiristanci to ba zaka tsani makwabcinka ba.” “Hakanan ba zaka je kana lalata kayayyakin gwamnati ba saboda kawai waɗanda ke kan madafun Iko sun gaza cika alƙawarin da suka ɗauka.”

“Mun koyar da rayuwa mai kyau a addinin mu na kirista, ba zai yuwu ka zama mai bin Allah ranar Lahadi kuma ka zama mai cutar wa ranar Litinin ba.”

A Martanin Aisha Yesufu ta bayyana cewar “Shugabannin addinai sun fi hatsari a kan shugabannin siyasa, sun maida mabiyansu tamkar bayi, kuma suna son shugabanci mara kyau domin cinikin farfagandan su.”

Labarai Makamanta