Malamai Da ‘Yan Siyasa Ne Silar Rashin Tsaron Najeriya – Sheikh Khalid

An bayyana cewar ko shakka babu halin taɓarɓarewar tsaro da Najeriya ke ciki musamman yankin Arewacin kasar, manyan ‘yan Siyasa da manyan malamai nada hannu dumu dumu a ciki, shi yasa matsalar ta ƙi cinyewa gaba ɗaya.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mashahurin Malamin Addinin Musuluncin nan Sheikh Muhammad Nuru Khalid, a yayin bikin kaddamar da wani littafi da aka yi a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis.

Sheikh Nuru Khalid ya yi ikirarin cewar wadansu daga cikin masu fada-a-ji wanda ya hada da ‘yan siyasa da Malaman addini, su ne asalin ma su daukar nauyin rashin tsaro a wasu sassa na kasar nan .

Sheikh Khalid ya yi ikirarin cewar ‘yan ta’adda wanda da yawansu matasa ne su na aikata ta’addanci ga al’umma sakamakon mu’amalarsu da sanannu malamai da ‘yan siyasa wadanda su ke son kasar ta kone kurmus.

Don haka ne ya yi kira ga gwamnati da ta yi gaggawar magance matsalolin Ilimi da rashin aikin yi, don a cewarsa, su ne silan rashin tsaron.

‘”Bata-gari sun yi kane-kane a harkar siyasar kasar. Su ne kuma wadanda su kewa tattalin arzikin karsar wasoso kuma su ke lalata rayuwar matasa. Hakazalika, tarbiya da ilimi sun tabarbare a kasar ta yadda ko matashi ya gama karatu, babu aikin yi” In ji Khalid.

“Yanzun haka babu wani daukan hankali da karatuttukan suke yiwa matasan sakamakon rashin kula da ma’aikata ke samu daga hannun gwamnati.

“Misali, likitoci su kenan tafiya yajin aiki lokaci bayan lokaci, wanda sai an magance irin wadannan matsalolin sannan Najeriya zata samu zaman lafiya.

“Har wayau, Gurbatattun mutane sune su ka kwace ragamar al’amurran addinai wadanda ke dasa kiyayya da rarrabuwan kai a zukatan mutane”

Khalid ya yi kira da gwamnati da kada ta yiwa ‘yan ta’adda wata rangwame sai dai idan akwai matsanancin bukatan hakan.

Labarai Makamanta