Makomar Najeriya: Kungiyoyin Arewa Sun Yi Kiran Kuri’ar Jin Ra’ayoyin Jama’a

Gamayyar kungiyoyin Arewa sun shigar da kara a gaban babban Kotun tarayya dake Abuja, inda suke bukatar a dakatar da Majalisar kasa kan batun yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulki, sannan a gudanar da kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a kan makomar kasa.

Da yake zantawa da manema labarai jin kadan bayan fitowa daga zaman saurarar karar a Abuja, mai magana da yawun Kungiyoyin na Arewa AbdulAziz Suleman, ya bayyana cewar sun shigar da Majalisar kasa da Ministan Shari’a kara ne, domin a dakatar da duk wani aikin gyaran fuska ga kundin tsarin mulki, a mayar da hankali domin tantance su wanene ‘yan Najeriya.

“A fili yake akwai wadanda ba su bukatar zama a Najeriya, a har kullum suna kiran kansu cewa su ba’yan kasa bane, misali kamar Inyamurai masu fafutukar kafa kasar Biafra da kuma Yarbawa masu hankoron kafa kasar Oduduwa, ya kamata a bar kowa ya kama gabansa kafin batun gyaran kundin tsarin mulki”.

Suleman ya ƙara da cewar wani abin farin ciki shine yadda aka samu wasu ayarin Lauyoyi daga sashin Kudanci wadanda suka bukaci a sanya su a cikin tsarin shari’ar, wadda za ta ba kowane bangare cin gashin kanshi.

An dage saurarar karar har ya zuwa ranar 20 ga watan Janairun shekarar badi ta 2022.

Labarai Makamanta