Makiya Ke Daukar Nauyin Yada Fastocin Tsayawa Takarata – Pantami

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, ya nesanta kansa da fastocin neman takarar shugaban ƙasa da wasu ke yaɗa wa a manyan biranen Nijeriya.

An ruwaito rahoto Sheikh Pantami ɗan asalin jihar Gombe, wanda tsohon darakta janar ne na hukumar NITDA, kafin daga bisa Buhari ya naɗa shi minista, na nuna tsananin damuwa da takaici dangane da wadannan fastocin da ake yaɗawa.

A baya-bayan nan ministan ya sha fama da kalubele kan matsayin Farfesa da jami’ar fasaha ta tarayya dake Owerri (FUTO) ta ba shi a fannin cigaban samar da tsaro a zamanance wato Cyber Security.

Bayan fastocin takarar shugaban kasa na Pantami sun watsu, ‘yan Jarida sun tuntubi hadimin ministan, Affan Abuya, kan sahihancin lamarin. Sai dai Mista Abuya ya yi watsi da lamarin baki ɗaya, inda ya bayyana cewa wannan na daga cikin aikin yan adawan ministan.

Hadimin Farfesa Pantami ya kara da cewa fastocin na karya ne kuma an kirkire su ne dan wata manufa daban amma ba da sanin Pantami ba. Yace: “Waɗan nan fastocin ba daga minista sadarwa suka fito ba, wata manakisa ce daga makiyan sa kawai.”

Labarai Makamanta