Ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta Action Alliance AA, Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya ce hukumomin da aka kirkira a Najeriya domin yakar cin hanci da rashawa ba za su iya yakar rashawan ba kwata-kwata.
Da yake zantawa da gidan talabijin na Channels a ranar Talata, tsohon hadimin na marigayi Abacha ya ce idan aka zabe shi shugaban kasa a shekarar 2023 shi zai inganta hukumomin dake yaki da rashawa a Najeriya.
“A Najeriya, na yi imanin cewa, hukumomin da aikinsu na farko shine kula da tsaro, cin hanci da rashawa a Najeriya ba su wadata ba. Suna da kaskanci sosai; basu da tsari mai kyau.”
Ya kuma bayyana cewa, daga abubuwan da yake gani kan yadda yaki da rashawa yake a Najeriya, kamar dai zomo ne ke bin zaki a guje a daji. Ya kuma koka da cewa, abin bakin ciki ne a ce hukumomin yaki da cin hanci da rashawa ba sa hada kai da sauran hukumomin kasashen waje don tsarawa da gano kudaden da aka ketarar daga Najeriya.
Al-Mustapha ya kuma ce, yana da kwarin gwiwa da kwarjinin iya tunkara tare da hukunta kowane dan rashawa ko ma wanene a kasar nan, ba tare da tsoro ko wata fargaba ba.
“Idan kuna maganan kwarjini ne, nagodewa Allah, ba wai ina alfahari bane.” Hamza Al-Mustapha ya ce bai taba satar kudi ba ko daukan arzikin kasa, sai dai ya kare dukiyar kasar duk da matsin lamba da wasu suka yi masa.
You must log in to post a comment.