Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamitin Bunkasa Tsaro

Majalisar Wakila a Tarayyar Najeriya, a ranar Laraba ta kafa wani kwamiti mai karfi da zai bullo da hanyoyin magance kalubalen rashin tsaro da ke adabar kasar ya kuma gabatar da rahotonsa cikin makwanni uku.

Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ne ya sanar da kafa kwamitin inda ya ce hakan na cikin abubuwan da aka amince da su yayin taron shugabannin kwamitin a safiyar ranar Laraba kafin fara zaman majalisa.

Kakakin ya ce kwamitin za ya kunshi dukkan shugabannin majalisar da kuma mambobi 30 daga jihohi 30.

Ya ce idan kwamitin ya kammala binciken za a mika wa Shugaba Muhammadu Buhari domin aiwatarwa.

Idan za a iya tunawa kalubalen tsaro kamar yan ta’adda, ‘yan bindiga, masu garkuwa da makasa na addabar mutane kuma an gaza samun mafita.

“Kwamitin za ya fara aiki nan take kuma za ya dauki kimanin watanni biyu ko uku kafin ya bada rahoton ta domin a mika wa shugaban kasa.

Kwamitin ya kunshi mambobi 30 da shugabannin majalisa,” in ji Gbajabiamila.

Labarai Makamanta