Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Gargadi Kan Yiwuwar Samun Rikici A Zaben 2023

Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS, sun gargaɗi Najeriya kan batun haddasa rikici a zaɓen ƙasar na 2023 da ke tafe.

Sun bayyana hakane a wani taron tattaunawa da kungiyar shiga tsakani na jam’iyyu da masu ruwa da tsaki da suka fito daga yankin arewa ta tsakiya da arewa maso gabas kan kaucewa tada fitina a Jos, babban birnin jihar Filato a ranar Talata.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce muddin ba a ɗauki mataki ba, za a iya samun rashin zaman lafiya a faɗin yankin.

Ita ma ECOWAS ta ce idan rikici ya ɓarke a Najeriya, babu wata ƙasa a yankin sahara da za ta iya bai wa ‘yan gudun hijirar ƙasar mafaka saboda yawansu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sama da mutane 30 ne aka ruwaito mutuwarsu yayin da da yawa suka jikkata a rikice-rikice gabanin zaɓen 2023 a sassan daban-daban na Najeriya.

An kuma kai wa ofisoshin hukumar zaɓe mai zaman kanta hare-hare a wasu sassa na Najeriya musamman ma kudu maso gabas, inda ake zargin kungiyar ‘yan awaren Biafra da kai hare-haren wanda ya yi sanadiyyar rasuwar jami’an INEC da kuma jami’an tsaro da dama.

Labarai Makamanta