Majalisar Dattawa Ta Shiga Firgici Da Labarin Kusantowar Boko Haram Abuja

Rahotanni daga Majalisar kasa Abuja na nuna cewa Sanatocin Najeriya a ranar Talata sun bayyana tsoro gami da fargaba akan labarin cewa mayakan Boko Haram na iya mamaye babban birnin tarayyar kasar Abuja nan bada jimawa ba.

‘Yan Majalisar Dattawan sun bayyana damuwar su a yayin zaman majalisar bayan wani kudiri, wanda Sanata Musa Sani daga jihar Neja ya gabatar.

Sanata Musa Sani wand ke wakiltar mazaɓar ɗan Majalisar dattawa ta Neja ta Gabas, ya sanar da takwarorinsa cewa tafiyar awa biyu ne kadai ke tsakanin yan ta’addan da Abuja.

“An watsar da mazaunan wadannan sassan jihar da ke fama da yaki kuma an barsu daga su sai halinsu wanda hakan ya tilasta masu zama cikin mummunan bakin ciki.”

Ya kara da cewa garuruwa 42 da ke fadin kananan hukumomin biyu na Shiroro da Munya sun fada karkashin ikon Boko Haram zuwa yanzu inda mazauna kauyuka kusan 5,000 suka rasa matsugunansu a cikin kwanaki uku da suka gabata.

Da yake bayar da gudummawarsa ga kudirin, tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu, a cikin nasa jawabin ya ce gwamnatin da Buhari ke jagoranta ta rasa cancantar ta na jagoranci.

“Duk gwamnatin da ba za ta iya kare rayukan mutane ba to ta rasa cancantar ta. Muna buƙatar yin wani abu game da wannan kuma cikin sauri. Idan akwai bukatar mu rufe jihar Neja ko majalisar dattawa domin neman mafita, to mu yi hakan.”

A matsayin hanyar magance matsalar, majalisar dattijai ta yanke shawarar tura shugabanninta don ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari. Shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya bayyana cewa zai jagoranci sauran manyan shugabannin majalisar dokokin, domin ganawa da shugaban kasa.

Labarai Makamanta