Majalisa Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Shirin Kidaya

Rahotanni daga Majalisar wakilai ta tarayya Abuja na bayyana cewar ‘yan majalisar wakilai sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗage kidayar jama’a da gidaje data shirya yi a shekarar 2021, nan take ba tare da ɓata lokaci ba.

Wannan kiran yazo ne bayan zauren majalisar ya karɓi kudirin ƙasa wanda ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Bosso/Paikoro a majalisar wakilai ta ƙasa daga jihar Neja, Shehu Beji, ya gabatar mata a zaman ta na ranar Laraba.

Yayin da yake gabatar da kudirin, ɗan majalisar yace, akwai dalilai da dama da zasu sa a dakatar da shirin kidayar waɗanda zasu shafi sakamakon da za’a samu bayan an kammala.

Ya ƙara da cewa samun nasarar wannan aikin na ƙidaya zai samu tasgaro sosai saboda matsalar tsaron da ‘yan Najeriya ke ciki a sassa daban-daban na ƙasar nan.

“Kodai wasu an tilasta musu barin matsugunin su ko kuma an kassara musu rayuwarsu ta yau da kullum.” inji shi. Sannan kuma Beji ya bayyana cewa babu tabbas ɗin masu ƙidayar zasu samu ingantaccen tsaro a mafi yawancin sassan ƙasar nan da matsalar tsaro ta shafa.

Labarai Makamanta