Majalisa Ta Ba Hafsoshin Tsaro Wa’adin Kawo Karshen Matsalar Tsaro

Rahotannin dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Majalisar Dattawa ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar Sanata Ahmed Lawan ta ba wa manyan hafsoshin tsaro wa’adin watanni hudu su kawo karshen matsalolin tsaron da ke addabar sassan kasar.

Wannan na zuwa ne bayan da majalisar ta yi wata doguwar ganawa da shugabannin a jiya, duk da cewa majalisar tana hutu.

A baya-bayan nan dai lamarin tsaro ya ƙara sukurkuce, al’amarin da ya kai ga wasu ‘yan majalisar yunkurin tsige Shugaba Muhammadu Buhari muddin bai sauya salo ba.

Majalisar dokoki ta bayyana tsoro da damuwarta game da ƙaruwar rashin tsaro a ƙasar, musamman harin da ƴan ta’adda suka kai kwanan nan a Abuja.

Shugaban majaliar Dattawa, Ahmad Lawan, ya kira shugabannin tsaro taron gaggawa a jiya, inda yace lamari ne mai ban tsoro.

A taron, sanatoci sun ba wa shugabannin tsaro shawarwari a kan yadda za a kare Birnin Tarayya da ƙasar gaba daya.

Mafi yawan kwamitocin majalisar dokokin su ma sun gana da shugabannin tsaro akan matsalolin tsaron a Juma’ar da ta wuce don sanin me ake ciki a ƙasar.

Majalisar wakilai ta ce ƴan ta’adda suna barazanar kai hari Abuja inda fadar shugaban ƙasa take, inda suka ce dole hukumomin tsaro su yi maganin masu tayar da ƙayar bayan.

A cikin makonnin da suka wuce, birnin tarayya ya fuskanci barazana daga wurin ƴan ta’adda akan kai hari kan wasu dakarun sojji da gidan yarin Kuje.

A ranar Alhamis ɗin da ta wuce ma, ƴan ta’adda sun kai wa sojojin da ke shingen bincike na Dutsen Zuma mai nisan kilomita kadan daga cikin birnin Abuja.

Labarai Makamanta

Leave a Reply