Majalisa Ta Amince Buhari Ya Ƙara Cin Bashi

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar majalisar dokokin tarayya ta amincewa mai girma Shugaban ƙasa Buhari da ya ciyo bashi mai nauyi domin cigaba da ayyukan raya ƙasa a Najeriya.

Majalisar dattawa ta amincewa gwamnatin tarayya ta karbi sabon bashin dalar Amurka dala Biliyan guda da rabi $1.5bn, da Miliyan 995 €995m daga kasashen waje.

A lissafin da aka buga, wannan kudi ya kama Naira Tiriliyan ɗaya da digo 1 N1.1tr a kudin Najeriya.

Sanatocin sun amince gwamnati ta karbi wannan bashi ne bayan kwamitin basussuka na majalisa ta gabatar da rahotonta kan shirin karban bashin gwamnatin tarayya.

Shugaban kwamitin, Sanata Clifford Ordia, ya gabatar da rahoton a gaban majalisa.

Labarai Makamanta