Majalisa Na Duba Yiwuwar Soke Yin Bautar Kasa A Najeriya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar Wakilai na duba yiwuwar dakatar da shirin bautar Kasa na NYSC, Kundin Tsarin Mulki na Tarayyar Najeriya na Canji shekarar 2020, wanda ke neman soke dokar NYSC, an gabatar da shi a karatu na biyu a gaban majalisar.

Wanda ya dauki nauyin yunkurin, Mista Awaji-Inombek Abiante, a cikin bayanin shawarar, ya zayyana dalilai daban-daban da za su sa a soke NYSC.

“Wannan kudirin yana neman a soke Sashi na 315 (5) (a) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya, 1999, (kamar yadda aka yi kwaskwarima) a kan wadannan dalilai:

“Kisan gilla ga ‘yan bautan kasa da ba su ji ba ba su gani ba a wasu sassan kasar saboda ta’addancin ‘yan bindiga, tsattsauran ra’ayin addini da rikicin kabilanci; yawan sace-sacen ‘yan bautar kasa da ake yi a fadin kasar; “Hukumomi da ma’aikatu na gwamnati da masu zaman kansu sun daina daukar matasa kwararrun ‘yan Najeriya aiki.

“Don haka sun dogara kacokan kan samuwar ‘yan yi wa kasa hidiman da ba a biyansu albashi mai tsoka kuma ake watsar da su ba tare da cimma komai ba a karshen shekarar su ba tare da fatan samun aiki ba; “Saboda rashin tsaro a duk fadin kasa, yanzu haka hukumar kula da bautar kasa ta fara tura ‘yan bautan kasa yankinsu, don haka ya saba daya daga cikin manufofin kafa kungiyar, watau bunkasa alakar da ke tsakanin matasan Najeriya da inganta kasa, hadin kai da hadewa.”

Hukumomin tsaro a Najeriya sun kuma ba da shawarar wuraren da ya kamata a kai ‘yan bautan kasa da kuma yankunan da ke da hadurra da basu dace a kai su ba.

Gwamnatin mulkin soja ta Janar Yakubu Gowon ta kafa NYSC ne a ranar 22 ga Mayu, 1973, a karkashin Doka mai lamba 24 ta 1973 a matsayin hanyar sasantawa da sake hada kan ‘yan Najeriya bayan yakin basasa tsakanin 6 ga Yulin 1967 da 15 ga Janairun 1970.

Labarai Makamanta