Maina Ya Rasa Beli A Karo Na Biyu

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar belin da Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa ya mika gabanta domin neman fita waje ganin likita.

Ana shari’ar Maina ne inda ake zarginsa da wawure kudi da suka kai naira biliyan biyu kuma ya daina halartar zaman kotu a watan Satumba, lamarin da ya jefa sanata Ali Ndume gidan gyaran hali.

An kama shi a jamhuriyar Nijar inda ya je neman mafaka kuma aka dawo da shi Najeriya a ranar 3 ga watan Disamban shekarar bara ta 2020.

Daga bisani an kwace belin Maina da aka bada kuma aka bukaci a cigaba da tsaresa a gidan gyaran hali har sai an kammala shari’arsa.

A wata bukata ta ranar 19 ga watan Fabrairu wanda Maina ya mika ta hannun lauyansa Sani Katu, ya bukaci a bada belinsa saboda halin rashin lafiya da yake ciki. Ya yi ikirarin cewa zai iya rasa kafarsa matukar aka hana shi zuwa neman magani.

A yayin zaman yanke hukunci a ranar Alhamis, alkali Okon Abang ya ce tsohon shugaban hukumar fanshon bai cancanci beli ba, saboda haka babu wannan maganar.

Labarai Makamanta