Shugaban majalisar malamai ta kasa na kungiyar Izalah Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi kira ga mawadatan da ke biyawa talakawa aikin hajji da su karkarta da kudaden nasu wajen siyawa talakawan ragunan layya wanda kuma ba shi da gidan kansa da su taimake shi su raba shi da gidan haya.
Sheikh Jingir ya kara da cewa a yanayin da ake ciki na rushewar tatttalin arziki sakamakon annobar corona, wasu talakawan da yawa ba za su iya biyan kudin haya ba saidai a kore su daga gidajen da suke haya.
Ya ce bana babu aikin hajji kuma akwai mawadatan da yawa da suke biyawa jama’a kudaden aikin hajji. Don haka ya ce kudin idan aka juya su za su siyawa talakawa da yawa gidaje su daina zaman gidan haya.
Sheikh Jingir yana wanan jawabin ne jiya yayin da yake gabatar da nasihar Juma’a a masallaci ‘Yan Taya dake birnin Jos jihar Filato.
A karshe ya yabawa shugaban kasa Muhammad Buhari bisa kudurinsa na gina gidaje masu sauki. Wanda za a rabawa talakawa ba shi. Inda ya yi kira ga ‘yan majalisu da su goyi bayan wannan tsarin, domin zai taimakawa talakawa da yawa.
You must log in to post a comment.