Maimaita Saɓo, Saɓo Ne Bana Goyon Bayan Muƙabala Da AbdulJabbar – Bauchi

Fitaccen malamin addinin musulunci kuma jigon dariqar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana bara’arsa ga zaman tattaunawan da gwamnatin Kano ta shirya yi da Abduljabbar Kabara da wasu malaman Kano.

Shehin Malamin ya nuna hakan a matsayin kuskure inda ya ce wasu malamai sun tafi a kan haramcin yi wa Mu’utazilawa martani, domin kafin martanin sai an maimaita abin da suka fada wanda hakan shi ma kuskure ne balle kuma Manzon Allah S.A.W.

” Misalin abin da yaron nan mara kunya Abduljabbar yake yi wa Annabi kamar uban da zai ga d’ansa na rigima da wani ne ya zo zai raba su sai yaron ya ce Baba ai ubanka ya zaga shi ya sa nake fada da shi. Sai Uban ya ce kai ne ka zage ni ba wanda kake fada da shi ba.” Inji Shehin Malamin.

Malamin ya ce” Bai dace a sake maimaita irin ‘batancin da Abduljabbar Kabara ya yi wa Annabi ba balle a saka shi kai tsaye a gidajen talabijin da gidajen rediyo wannan tamkar wasa ne da mutuncin Annabi S.A.W. don haka muke kira ga hukuma da ta janye taron nan sharri za a yada wanda bai ji ba ma ya ji. Ba kowanne musulmi ke da imani ba. Wanda bai da imani idan yaji zai iya cewa ashe haka Annabin yake dama?

Don haka muna goyon bayan rushe makarantarsa da masallacinsa. Hukuma na da ikon rushe masallaci ko makarantar da ake zagin Annabi S.A.W. muna godiya ga Kotu da gwamnatin Kano da ta ce za ta yi biyayya ga umarnin Kotu. Ba wanda zai so a shiga gidan rediyo a dinga fadin munanan kalamai a kan babansa da sunan labari ake bayarwa ana ba shi kariya. Balle fiyayyen Halitta SA.W.

Raina martabar Annabi komai kankantarsa babban laifi ne. Irin maganganun da yaron nan Abduljabbar yake yi na ‘batanci ga Annabi ba su da dadin ji sai ya dinga kirkirar munanan abubuwa da sunan kare Annabi.

Manzon Allah Uba ne ga kowanne mumini. Haka matansa ma iyayen muminai ne. Don Annabi ya kawo sahabbai ‘ya’yansa gidansa suna cin abinci sai a dinga mummunan tunani ? Don wata Mata ta ce ta na son ta kebe da Annabi S.A.W su yi magana wanda yake mahaifi a gare ta sai a yi mummunan tunani? Raina manzon Allah ne ya sa suke wannan mugun tunani. Akwai hadisin da ke bayyana duk abin da Manzon Allah ya fada ko abin da ya aikata ko abin da aka aikata a gabansa bai hana ba dukkansu hukunci ne a musulunci domin manzon Allah shi ne mai shari’a. Don haka babu kyau maimaita irin munanan kalamai da wannan yaro mara kunya yake fada ga janibin Annabi Sallallahu alaihi wa sallam.” Inji Shehu Dahiru Bauchi.

An jima ana zargin Abduljabbar Kabara da aikata ‘batanci ga janabin Manzon Allah S.A.W tare da matansa da sahabbansa wanda hakan ya janyo gwamnatin Kano dakatar da shi daga hawa mumbari.

Labarai Makamanta