Mahajjata Dubu 65 Ne Za Su Gudanar Da Aikin Hajjin Bana Daga Najeriya

Hukumar Alhazan Naijeriya NAHCON tace jiragen sama sun yi sawu 93 da maniyyata aikin hajji daga jihohin Naijeriya dubu 44,450, da na fasinjojin jirgin yawo dubu 20, 550, Wanda jimillar Alhazan ya kai adadin mutum dubu 65000 zuwa kasa mai tsarki.

Jirgi na karshe ya tashi a ranar Talata daga birnin tarayya Abuja dauke da maniyyata 301 wadanda basu samu tafiya ba daga sassan Nijeriya. Kazalika ma’aikatan hukumar Alhazan NAHCON sun bar Nijeriya a ranar talatar bayan tabbatar da cewa dukkan maniyyata sun samu tafiya.

Shugaban hukumar Barista Abdullahi Mukhtar ya jinjina wa kamfanonin jiragen saman da suka yi jigilar Alhazan bisa hadin kai da suka bayar duk da kalubale da aka fiskanta. Haka kuma ya jinjina wa shugabannin hukumar jindadin Alhazai na jihohi bisa kokarin su da jajircewar su.

Hukumar ta jinjina wa dukkan masu ruwa da tsaki da suka bada gudunmawar su don ganin aikin ya tafi yanda ya dace.

Related posts