Magance Matsalar Tsaro: An Bar Jaki Ne An Koma Dukan Taiki – Shugaban DSS

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar jami’an tsaro na farin kaya DSS, ta ba gwamnatin tarayya shawarwari akan hanyoyin samar da zaman lafiya da tsaro a garuruwa, domin fita daga halin ƙuncin da ake ciki.

Shugabn hukumar ‘yan sandan farin kaya, Yusuf Bichi, wanda ya yi jawabi a taron 2021 Ugwumba Enterprise Challenge, ya ce musamman idan aka mayar da hankali kan matasa da matsalar kyarar mata, Najeriya za ta samu zaman lafiya.

Bichi wanda ya samu wakilcin kakakin DSS, Peter Afunanya, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta hada kai da mutane da kungiyoyin da za su janye hankalin matasa daga tituna don basu abubuwan yi.

Abinda Ugwumba Leadership Centre take yi shine tabbatar da matasa sun dogara da kawunansu musamman a bangaren kudi don taimaka wa gwamnati wurin shawo kan rashin tsaro. Ya ce matsawar aka shawo kan matsalolin matasa da mata an gama da matsalar rashin tsaro.

“Idan ka gama da matsalolin matasa ko kuma ka shawo kan matsalar wariya da kyarar mata, ka gama da batun rashin tsaro. “Misali, kamar yadda muka sani, kasar mu tana fama da rashin tsaro, ba kuma a Najeriya kadai bane, gaba daya duniyar ce, kasashe da dama su na da irin wadannan matsalolin.

Labarai Makamanta