Magance Hatsari: Hukumar Kiyaye Hadura Ta Yi Wa Direbobi Bita A Abuja

Daga Muhammad Sani Yusuf Nassarawa

Akokarin da Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa Reshen Babban Birnin Tarayya Abuja keyi na wayar da kan Direbobin Mota don Kaucewa Tukin Ganganci da Kuma kaucewa daukar Mutane ko kayan da ya Wuce Kima.

Hukumar kiyaye Hadurran na yankin Zuba sun Shirya wani taron Ganawa da Direbobin J5 dake Wannan yanki Domin Tattauna matsalolin da kuma hanyar magancesu

Da take Jawabi a Wurin taron Babbar Kwamandan dake kula da yankin Zuba na Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa Elizabeth Benedict tace Sun Shirya Taronne Domin fadakar da Direbobin akan kiyaye kaidar Tuki da kuma Fahimtar Juma Sanna ta bada marnin Duk Direban da aka kama yana dauke da dabbobi ko kuma wani kayan da ka iya lalacewa yaje ya sauke kayan tuna kafin adawo da motar domin bai kamara hukumarsu tayi sanadiyyar mutuwar dabba ko lalacewar kayan masarufi ba

Shima a nasa jawabin Kwamandan da ke kula da yankin Dei Dei na Rundunar Tsaro ta Civil Defemce Muhammad BALA yace ya zama wajibi ga masu keke napep da sauran masu daukar kayan da ya wuce kiima su daina sannan ya tabbatar da duk wanda ya saba kaida to doka za tayi aiki a kansa hakanne yasa aka ahirya taron don samun fahimtar Juna da kuma aiki tare

Wasu daga cikin Direbobin da Mahalarta taron sun nuna damuwarsu akan yadda jamian hukumar ke matsa musu lamba akan abinda bai taka kara ya karya ba
To saidai wannan koken tuni Hukumar ta basu hakuri sannan tace zata Duba kuma za a ga sauyi a tsakanin Jamian nata duk da cewa baza a rasa bara gurbi ba a kowacce irin Hukuma na kasarnan dama su kansu Direbobin

shima Kwamandan dake Kula da shiyyar Abuja Ochi Samuel Oga, ya yi Godiya ga Direbobin da irin hadin kai da suke bayarwa inda yace kofarsa a bude take garesu domin gabatar da korafe korafensu kuma yasha Alwashin Taimaka musu aduk Lokaci da Bukatar Hakan ta taso

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa dai na Gudanar da Gangami a Kowacce watannin hudun karshen shekara wadanda ake shewa ember month domin jan hankalin Direbobi dangane da kiyaye kaidar Tuki

Labarai Makamanta