Mafi Yawan ‘Yan Arewa Munafukai Ne – Naja’atu Muhammad

Gogaggiyar ‘yar siyasarnan, Hajiya Naja’atu Muhammad ta caccaki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, inda ta ce gwamnatin Buhari a baibai ta ke tafiya, Sannan ta bayyana ‘yan arewa a matsayin makwadaita kuma munafukai sanan ga tsoron tsiya.

A wata hirarta da gidan Rediyon RFI Hausa Naja’atu ta ce; “.Duk Gwamnati a duniya babban aikinta shi ne wannIta kasa kare rayuka da dukiyoyin al’umma, ba gwamnatin ba hukuma, ba ta da amfani.”.

“wannan gwamnatin ba ta yi wa al’umma amfanin komai ba don ta kasa kare musu dukiyoyinsu da rayukansu”.

Hajiya Naja’atu wacce ma’aikaciya ce a maikatar kula alamuran ‘yansanda ta ci gaba da cewa; “ba a rasa (masu fada mata gaskiya ba), ko mu muna fada. Yanzu ma fada muke, Rayukan mutumin arewa ya zama ba shi da amfani. Mafi yawan mutanen Arewa munafukai ne, mafi yawansu matsorata ne, mafi yawansu makwadaita ne!

‘Yan siyasar arewa banda tumasanci da karya da sata ba sa komai. Sun shiga siyasa ne ba don al’umma ba sai don su cika aljihunsu. Ana kashe ‘yan arewa kamar kiyashi. Banda a arewa ba inda za a yi wannan a zauna lafiya”.

Sannan ta ce“Gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta tausayin al’umma, musamman al’ummar arewa, saboda sun yi shiru. Duk idan ka yi shiru ka yarda ke nan. Kashe mutane shi ne kudi a wurin sojojin Nijeriya, shi ne kudi a wurin ‘yan sandan Nijeriya.

Labarai Makamanta