Mafarauta Za Su Iya Dakile Matsalar Tsaro A Najeriya – Yahaya Bello

Rahotannin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya roki yan majalisun tarayya su gaggauta amincewa da kudirin mafarauta 2020 ya zama doka, domin ganin bayan matsalar tsaro a Najeriya.

Kudirin wanda ya tsallake karatu na ɗaya da na biyu a dukka majlisun tarayya biyu, sanata mai wakiltar Ekiti ta kudu, Biodun Olujimi, shine ya gabatar da shi.

Gwamna Bello ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin ƙungiyar mafarauta ta Najeriya a Abuja ranar Asabar, Bello yace mafarauta zasu taka rawar gani wajen taimaka wa gwamnatin tarayya a yaƙin da take da matsalar tsaro.

A cewar gwamnan ɗaya daga cikin manyan dalilin da yasa gwamnatinsa a Kogi ta samu nasarar dakile aikata manyan laifukan ta’addanci shine amfani da mafarauta.

Gwamnan yace: “Zan roki majalisar tarayya ta yi saurin amincewa da kudirin mafarauta ya zama doka domin hakan zai bamu damar ɗaukar ku aiki baki ɗaya.” “Kuna ganin yadda mafarauta suke yi a jihar Kogi, wani lokacin ma suke zuwa su ceto jami’an tsaro idan rana ta baci.

Idan kowane inci na ƙasa kuna wurin, to zaku kare shi. “Idan kuwa muka kare kowane inci na kasa, to kauyukan mu zasu zauna lafiya, kananan hukumomi, jihohi, hatta ƙasar mu zata samu zaman lafiya.”

Daga ƙarshe gwamnan ya gode wa mafarautan bisa nuna goyon bayansu ga takararshi a 2023, tare da tabbatar musu da cewa za’a tafi da su.

Labarai Makamanta