Madugun ‘Yan Zanga-Zanga Sowore Ya Sha Harsashi A Abuja

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ‘Yan sanda a babban birnin sun harbi mawallafin jaridar Sahara Reporters kuma tsohon dan takarar shugaban kasa yayin wata zanga-zanga a bakin Unity Fountain dake a Abuja.

An harbi Sowore a gefen dama a cinya lamarin da ya sa aka yi gaggawan wucewa dashi asibiti domin ceto ranshi.

Madugun ‘yan Zanga-Zangar ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewa: “Yanzun nan ‘yar sanda, ACP Atine ta harbe ni a Unity Fountain a Abuja.

Zanga-Zangar #RevolutionNow Yanzu aka fara gwagwarmaya za ta ci gaba koda kuwa za su dauki raina!” Inji shi.

Labarai Makamanta