Maciya Amanar Ƙasa Zasu Gwammace Kiɗa Da Karatu – Bawa

Sabon Shugaban Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC Abdulrasheed Bawa, ya ce a karkashin jagorancinsa, hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa za ta himmatu wajen yaki da cin hanci da rashawa, ba tare da nuna sani ko sabo ba.

Da yake jawabi a ranar Juma’a lokacin da ya hau kujerar a hukumance, Bawa ya yi alkawarin jan ragamar hukumar zuwa ga bin diddigi da binciken sirri. Ya ce zai kirkiro da cikakken iko na hukumar leken asiri da za ta jagoranci tattara bayanan sirri, wadanda zasu tabbatar da kwararan matakan yaki da cin hanci da rashawa.

Bawa ya kuma yi alkawarin sauya fasali a tsarin hukumar na yaki da cin hanci da rashawa, wanda zai mai da hankali kan yaki da rashawa, ba mutane ba.

“Zamu zamanantar da ayyukan mu, kuma zamu kirkiro da wani sabon shugabanci mai cikakken iko wanda zai bamu damar tattara bayanan sirri ta yadda zamu zama masu himma wajen yakar laifukan tattalin arziki da na kudi.
“Kuma ta yin hakan, za mu kuma bai wa gwamnati shawarwari masu inganci da za su haifar da kyakkyawan shugabanci,”.

“Akwai bambanci tsakanin fada da cin hanci da rashawa da fada da mutane masu rashawa; kuma a ci gaba, za mu kasance masu himma wajen yaki da laifukan tattalin arziki da na kudi.

“Ga abokan hadin gwiwarmu da ke fadin kasar nan, za mu ci gaba da aiki tare da ku. Za mu ci gaba da musayar bayanan sirri, don ganin an dawo da dukiyar da aka sace ta kasar nan don ci gaban mu baki daya.

“Amma duk wadannan, za mu yi su ne kamar yadda aka san EFCC da yin abubuwan ta. Abubuwan da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya da dokokin kasar nan suka shimfida, sun kasance sune jagora a garemu.”

Bawa ya karbi aiki ne daga hannun Mohammed Umar wanda ke rike da mukamin tun watan Yulin shekarar 2020 bayan dakatar da Ibrahim Magu, tsohon shugaban riko na hukumar, kan zargin cin hanci da rashawa.

A lokacin mika jawabin, Umar ya bayyana kwarin gwiwar cewa Bawa zai gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.

Labarai Makamanta