Mace-Macen Kano: Akwai Lauje Cikin Nadi

Bana raba dayan biyu, idan har akwai wani dan Kano dake karanta wannan dan takaitaccen rubutu nawa zai ji na sosa masa in da ke masa kaikayi, ku daure ku bani aron kunnuwan ku.

Sanannan abu ne a kusan kowacce shekara lokacin shigowar damina tsakanin watan Aprilu da Maris akan samu yawaitar zazzabin cizon sauro a jihar Kano, a irin wannan lokaci duk in da ka zaga asibitoci da dakunan shan magani na Chimist-Chemis a unguwanni musamman da daddare mutane zaka tarar jingim, da sukan je domin ganin likita.

Bana mantawa zazzabin bara duk da babu annobar Coronavirus sannan asibitoci na aiki ka’in da na’in, haka yayi ta kamari har wani suna aka rika kiran sa dashi, wato (Abba gida-gida), sunan wani tsohon dan takarar gwamnan Kano da yayi matukar shuhura, ba kuma komai ne yasa ake kiran zazzabin da wannan suna ba sai saboda yadda yayi ta shiga kowanne gida, kuma duk lokacin da ya shiga wani gida kusan kowa sai yayi jinya. Allah yasa dai kun tuna !.

Masana lafiya da dama sun yi ta alakanta wannan zazzabi na shekara-shekara da ake samu a wasu jihohin arewacin Najeriya musamman Kano da sauyin yanayi, wato yayin da ake kokarin fita daga lokacin zafi don shiga damina.

Toh yau kuma sai Allah ya kaddara lokacin shi wancan zazzabi da a bara aka rika kira Abba gida-gida ya zagayo a lokacin annobar Korona, cutar da ba’a taba ganin irin ta ba a tarihi, in banda zamanin Spanish Flue a 1918, da kuma Black Death wacce duk in da ta shiga sai ta lakume rayukan rabin mutanen garin kamar yadda masana tarihi ke bada labari.

Ina son mai karatu ya daure ya amsa wa kansa wadannan tambayoyi biyar da zan jero a kasa.

(1 ) Me zai faru idan har mara lafiya bazai samu abin hawa ko motar hayar da zata kai shi zuwa asibiti a lokacin da yake fama da tsananin rashin lafiya ba saboda an saka dokar hana zirga-zirga ?.

(2) Me zai faru idan har likitoci na tsoron taba marar lafiya saboda tsoron ko yana dauke da Coronavirus ?.

(3) Me zai faru idan har hukumomi sun karkata hankalin su akan cutar Coronavirus alhalin akwai wasu dake fama da wata rashin lafiyar ta daban ?.

(4) Me zai faru Idan har su kansu wasu daga cikin jama’a na tsoron kai kansu zuwa asibiti saboda kada ace suna dauke da cutar Coronavirus ?.

(5) An bada rahoton cewa wasu asibitocin a Kano na gwamnati da ma masu zaman kansu sun bukaci marasa lafiyan dake kwance a cikin su, da su koma gida saboda fargabar kada a samu yaduwar cutar Coronavirus, idan sun je gida wa zai kula da lafiyar su a can ?, me zai faru idan akace an salami marar lafiya a lokacin da bai warke ba ?.

Zan barku da amsoshin wadannan tambayoyi, sai dai kafin hakan bari in barku da wata karin maganar Mallam Bahaushe, dake cewa ‘’Mai hankali ne kadai ke gane furfurar tinkiya’’.

Daga : Edita.

Related posts