Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Za Su Koma Aiki Bayan Hutun Shekaru Biyu Na Korona

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar bayan watanni 20 suna zaune a gida tun bullar cutar Korona a Najeriya, gwamnatin tarayya ta ce ma’aikata dake daraja ta 12 da abinda yayi kasa su koma bakin aiki ranar 1 ga Disamba, 2021.

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan ta bayyana hakan a takardar da ta fitar mai lamba HCSF/ 3065/ Vol. 107.

Ta bayyana cewa bisa shawarar Kwamitin fadar shugaban kasa dake yaki da annobar Korona, Shugaba Buhari ya wajabtawa dukkan masu niyyar dawowa yin rigakafin Korona.

Idan ba a mance ba tun watan Maris 2020, gwamnatin tarayya ta umurci ma’aikatan gwamnati masu darajar ta 12 da abinda yayi kasa su rika aiki daga gida domin rage yaduwar cutar.

Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa duk ma’aikacin gwamnatin da bai yi rigakafin Korona nan da ranar 1 ga Disamba ba, ba zai samu damar shiga ofishinsa ba.

Sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana hakan ranar Juma’a a Abuja yayin taron kamfen yiwa mutane rigakafin. Ya yi kira ga ma’aikatan gwamnati su ribaci kwanaki goma da suka rage cikin watan Nuwamba wajen yin rigakafin.

Labarai Makamanta