Ma’adinan Karkashin Kasa Dake Arewa Ne Silar Ta’addanci A Yankin – Kwankwaso

Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar Jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, yace fafutukar neman ma’adan kasa ne asalin abinda ya haifar da ta’addanci a arewa maso yamma da arewa maso gabas.

Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a Chatham House da ke birnin Landan na ƙasar Burtaniya ranar Laraba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Ministan tsaro yace mutane daga ciki da wajen Najeriya ke “Satar” ma’adanai shiyasa yaƙi ya turnuke yankunan.

“A ƙasata Najeriya muna da tsarin lada da kuma tsarin hukunci saboda a halin yanzun komai ya wuce. Lokacin ina gwamnan Kano, ba wanda zai je da sunan gwamnati ya karbi harajin ƙwandala ɗaya.” “Tsawon shekaru 8 da na kwashe kan madafun iko ban karbo bashin ko kwabo ba, abinda muka maida hankali shi ne albarkatun jiharmu, shiyasa wasu mutane ke tambayar wai ina muke samun kuɗin shiga.”

“Yaƙe-yaƙen da ake a arewa maso yamma da arewa maso gabashin Najeriya duk kan ma’adanan ƙasa ne, mutane na sace su daga cikin Najeriya da waje, ciki harda Gwal da sauran ma’adanai.” Kwankwaso ya ce lokacin ya yi da wannan matsalar zata kau, gwamnati ta ƙwace wadannan Arzikin da Allah ya bamu domin yi wa yan kasa aiki.

Bugu da kari, tsohon gwamnan yace Najeriya ta wayi gari cikin wannan bakin yanayin ne sakamakon gurbataccen shugabanci da kuskuren zabe.

Labarai Makamanta