Lokaci Ya Yi Na Daukar Matasa 774,000 Aikin Yakar ‘Yan Bindiga – El Rufa’i

Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai na Jihar Kaduna ya shawarci gwamnatin Najeriya ta ɗauki matasa 1,000 daga kowace ƙaramar hukuma aikin bayar da tsaro don yaƙar ‘yan fashin daji masu garkuwa da mutane.

Da yake magana jim kaɗan bayan miƙa masa rahoto kan matsalar tsaro a jihar ranar Laraba, El-Rufai ya ce babu wata hanyar yaƙi da ‘yan fashin daji illa “yi musu ruwan wuta a lokaci guda”, abin da ya sa yake son a ɗauki matasa 774,000 aikin.

“Ina kira ga jihohi 36 da su ɓullo da wani shirin gaggawa na ɗaukar mutane aiki a rundunonin tsaro. Gwamnati ka iya sauya halin da ake ciki idan ta ɗauki matasa 1,000 aiki daga kowace ƙaramar hukuma a faɗin ƙasa.

“Hakan zai zama gagarumin adadi na dakaru a fagen daga tun bayan yaƙin basasa. Adadin sabbin dakaru 774,000 a filin yaƙi zai kasance babbar hanyar gamawa da miyagu da kuma samar da aikin yi.”

Kazalika, gwamnan ya nemi gwamnatin Shugaba Buhari ta ayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda “saboda sojoji su samu damar kashe su ba tare da wata matsala ba”, in ji shi.

“Mu a Kaduna mun sha neman a ayyana ‘yan fashin nan a matsayin ‘yan ta’adda. Mun rubuta wasiƙu ga gwamnatin tarayya tun 2017 muna neman a yi hakan saboda ayyana su ne kaɗai zai bai wa sojoji damar karkashe waɗannan ‘yan fashin ba tare da wani abu ya biyo baya ba daga ƙasashen duniya.”

Sabon rahoton da aka gabatar wa El-Rufai a yau ya nuna cewa mutum 343 aka kashe a Kaduna daga 1 ga watan Yuli zuwa 30 ga Satumban 2021 sakamakon ayyukan ‘yan fashi da kuma rikicin ƙabilanci a jihar.

Haka nan, ‘yan fashin dajin sun sace mutum 830 cikin wata ukun da rahoton ya bayar da bayanai a kai tare da raunata 210.

Labarai Makamanta