Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya ce lokaci ya yi da za a cire batun addini daga siyasar ƙasar nan tare da hukunta ‘yan siyasar da ke amfani da addini a matsayin makamin yaƙin neman zaɓe.
Rahotanni sun ambato Gwamnan na wannan maganar ne a ranar Talata a Kaduna lokacin bikin ƙaddamar da babban ofishin ‘gidauniyar zaman lafiya da ci gaba’ ta mai alfarma sarkin musulmi
El-Rufai ya yi kira ga Sarakunan gargajiya da malaman addini da su riƙa gudanar da addu’o’in samun ingantaccen zaɓe da samun zaman lafiya a fadin ƙasar.
Ya ce “Ina so na yi amfani da wannan damar na yi kira ga shugabanninmu da ke nan, masu girma sarakunan gargajiya da malamanmu da su ci gaba da yi wa ƙasarmu addu’o’in samun zaman lafiya da samun ingantaccen zaɓe, tare da yin addu’ar Allah ya zaɓa wa ƙasarmu shugabannin na-gari da za su haɗa kan ƙasar tare da ciyar da ita gaba”
”A matsayina na ɗan ƙasa, kuma gwamna sannan kuma musulmi bana jin daɗin yadda wasu ‘yan siyasa ke amfani da addini da ƙabilanci a matsayin makaminsu na yaƙin neman zaɓe”, in ji El-Rufai.
Haka kuma gwamnan ya ce lokaci ya yi da za a cire batun addini daga siyasar ƙasar tare da hukunta waɗanda ke ƙoƙarin amfani da addinin a matsayin makamin yaƙin neman zabe.
You must log in to post a comment.