Lokaci Ya Yi Da Matasa Za Su Amshi Mulkin Najeriya – Abdulkarim

An bayyana cewar lokaci yayi da matasa a tarayyar Najeriya zasu mike wajen amshe ragamar mulki a hannun Dattawan kasar nan, duba da yadda Dattawan suka gaza wajen ciyar da kasa gaba.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin wani mai nazari da fashin baƙin al’amura a Najeriya mai suna Ibrahim Abdulkarim, lokacin da ake zantawa dashi a cikin wani shiri na gidan talabijin na Liberty “States Of The Union” a karshen mako.

Ibrahim Abdulkarim ya zargi Dattawa wadanda suka yi kane-kane akan madafun ikon ƙasar nan da cewa, sune silar lalacewar komai kasar sakamakon rauni da suke dashi na jagoranci.
Kuma haka za’a cigaba da tafiya matukar matasa a kasar basu mike wajen kwato ‘yancin su daga halin da ake ciki ba.

Abdulkarim ya cigaba da cewar a yanzu ya bayyana a fili cewa, hanyoyin da Dattawan Najeriya ke bi wajen gudanar da sha’anin mulki ba masu ɓullewa bane, bisa ga haka Matasa ba zasu cigaba da rungume hannu suna kallon ƙasa na fuskantar koma baya ba tare da ɗaukar matakan da suka dace ba.

“Muna ta ƙoƙarin wayar da kan Matasa a Najeriya da su tashi tsaye, su yi rijistar zabe da kawar da duk wata jam’iyya da bata ba matasa damar taka rawa a cikin ta ba.

Ibrahim Abdulkarim ya tabbatar da cewar matasa ne kaɗai zasu tsamar da Najeriya daga halin da ta tsinci kanta a ciki, domin muddin kida ya canza ya zama wajibi rawa ya canza.

Labarai Makamanta