Likitoci Sun Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki

Ƙungiyar likitoci ƙasar nan sun yi barazanar zasu tsunduma yajin aiki matuƙar gwamnatin ƙasar nan bata biya musu buƙatunsu ba.

Ƙungiyar tace zata saurari gwamnati daga nan zuwa ɗaya ga watan

Afrilu idan ba’a biya musu buƙatun su ba zasu shiga yajin aiki, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar bayan babban taron ta na ƙasa, ƙungiyar ta bayyana cewa buƙatun nata sun haɗa da biyan likitoci albashin su da aka riƙe.Da kuma biyan albashin watan Maris da muke ciki kafin 31 ga watan Maris ɗin.

Sauran buƙatun sun haɗa da: biyan mambobin ƙungiyar hakkoƙin su da suke bin bashi harda na watan Maris musamman na jihohi da kuma ma’aikatan lafiya na makarantun gaba da sakandire.

Da kuma biyansu kuɗaɗen su na aikin haɗari da suke yi, 50% na asalin albashin ma’aikatan lafiya da kuma kuɗaɗen su na COVID19 musamman a jihohin ƙasar nan.

Ƙungiyar likitocin na cikin gida NARD ta kuma yi kira da a canza shugaban likitoci na (MDCN) saboda gazawar sa wajen gudanar da aikinsa yadda ya kamata.
Hakan zai bada cikakkiyar damar aiwatar da gyaran tsarin likitocin cikin gida ba tare da wani tsaiko ba.

NARD ta kuma kara yin kira da biyan ragowar albashinsu na shekarun 2014, 2015 da kuma 2016 ga mambobinta dake makarantun gaba da sakandire, na jihohi, kamar yadda a kayi yarjejeniya da su a baya.

Hakanan kuma ƙungiyar ta yi kira da a biya kuɗaɗen inshora na ma’aikatan da suka rasa rayukansu a bakin aiki musamman waɗanda suka rasu saboda kamuwa da cutar korona.

Sannan kuma likitocin na buƙatar a gaggauta biyan kuɗaɗen bada horo na shekarar 2020 da 2021 ga mambobinta harda waɗanda ke aiki ƙarƙashin gwamnatocin jihohi.

Labarai Makamanta