Likitoci Sun Bukaci Sanya Hannu A Dokar Kare Hakkin Mata

Ƙungiyar likitoci masu lura da lafiyar mata ta ƙasa ta buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya sanya hannu kan dokar kare lafiyar mata da jarirai.

A cewar ƙungiyar hakan zai zamo wani abin tarihi, wanda al’ummar ƙasar ba za su manta da shi ba.

Shugaban ƙungiyar, Dr Habib Sadauki ne ya buƙaci hakan a wata ganawa da ya yi da manema labarai ranar Lahadi.

Sadauki ya ce dokar za ta taimaka wajen rage mutuwar mata masu juna-biyu da jarirai.

Ya ƙara da cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen da har yanzu suke da mafi yawan alƙaluma na mace-macen masu ciki da kuma jarirai.

Labarai Makamanta