Legas: Hukumar EFCC Ta Yi Nasarar Damke Janar Na Bogi

Labarin dake shigo mana daga Birnin Ikko na jihar Legas na bayyana cewar Hukumar EFCC ta kama wani sojan bogi mai muƙamin Manjo Janar inda aka kama shi bisa zargin zamba ta naira miliyan 270.

Hukumar ta EFCC ta kama Bolarinwa Oluwasegun wanda ya yi iƙirarin cewa Shugaba Buhari ya zaɓe shi a matsayin shugaban sojojin ƙasa na Najeriyar.

Mista Bolarinwa ya roƙi wani kamfani na Kodef Clearing Resources da ya ba shi kuɗi domin a tabbatar da shi a matsayin shugaban.

Haka kuma ana zarginsa da yin wata takarda ta bogi da sa hannun shugaban Najeriya wadda ke nuna iƙirarin da ya yi na zaɓar shi domin shawo kan kamfanin ya ba shi kuɗin.

Labarai Makamanta