Lauyoyin jagoran ‘yan a-ware Biafra, Nnamdi Kanu, sun ce sun fara daukar matakin shari’a kan gwamnatin Najeriya da Kenya a hukumar kare hakkin dan adam ta Tarayyar Afirka, AU.
Sun bukaci kasashen biyu su yi bayani dalla-dalla kan zargin tasa keyar wanda suke karewa zuwa gida ba tare da bin ka’idojin da suka dace ba.
A wata sanarwa da babban lauyan Mista Kanu, Alloy Ejimako ya fitar, ya ce sun kai batun gaban AU ne saboda dukkan kasashen biyu mambobi ne na hukumar kare hakkin dan adam ta Tarayyar Afirka.
Lauyoyin Kanu sun bukaci a mayar da shi kasar Kenya kuma a matsayin dan Birtaniya, tare da zargin cewa kama shi da aka yi ya saba wa doka.
Nnamdi Kanu dai yana da shaidar zama a Birtaniya, kuma har yanzu babu wani cikakken bayani kan yadda aka taso keyarsa zuwa Najeriya a watan ya gabata.
Gwamnatin Kenya ta musanta hannu a kama shi da mayar da shi gida Najeriya.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Najeriyar ta gagara gabatar da Mista Kanu a gaban kotu, domin ci gaba da shari’ar da ake masa kan zarge-zarge masu alaka da cin amanar kasa da aikata ta’addanci.
Wata babbar kotu a Abuja da ke zaman sauraren karar, ta dage shari’ar har sai ranar 21 ga watan Oktoba mai zuwa.