Lauyan Igboho Ya Fallasa Halin Kunci Da Yake Ciki

Babban lauyan mai rajjin kare hakkin Yarbawa Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bayyana irin mummunan halin da wanda ya ke karewa ke ciki a hannun yan sandan Jamhuriyar Benin inda ake azabtar dashi tamkar dabba.

Cif Yomi Aliyu (SAN) ya bayyana hakan ne yayin da ya yi magana da manema labarai a daren ranar Talata.

Ya ce ƴan sandan na Jamhuriyar Benin sun kama Ropo, matar Sunday Igboho, sun ajiye ta a wani ɗakin ajiye wadanda ake zargi da laifi. Ya ce: “Sun ɗaure shi da mari a inda aka ajiye shi a Cotonou.

Anyi hayaniya a filin tashin jiragen sama a lokacin da aka kama shi. Sun buge shi a hannu sannan suka saka masa ankwa a hannun, yana cikin azaba kuma yana ta sharɓar kuka tamkar yaro ƙarami a lokacin da na kira shi, na ji shi.

“Ita ma matarsa an saka ta a wani ɗaki daban amma ba a saka mata mari ba, ita ma matar tana kuka saboda yana cikin azaba. Muna addu’ar kada su biya wani ya kashe shi. Ba daidai bane ka rufe mutum sannan ka saka masa mari.

“Kun san ya ji ciwo amma ba ku kai shi asibiti ba. Mun ji cewar za a gurfanar da shi a kotu gobe ba mu san ko hakan zai yiwu ba.”

Labarai Makamanta