Lalacewar Makaratu: Malaman Jinya Da Anguwan Zoma Sun Yi Zanga-Zanga A Taraba

BASHIR ADAMU, JALINGO.

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Taraba yanzu na cewa, biyo bayan cigaba da tabarbarewan da Makarantar koyar da Jinya da Anguwan Zoma na Jihar Taraba wato (Taraba State College of Nursing and Midwifery) na zaman Makokin Sati guda saboda tsananin lalacewar da Makarantan tayi da zaman alhini bayan shekaru biyar da rasuwan wanda ya gina Makarantan don cigaban Al’umman Jihar Taraba, Marigayi Danbaba Danfulani Suntai.

A cewan Malaman Makarantar, zaman makokin Sati gudan da suka fara shine don Addu’a dauki daga wurin Ubangiji Allah daya kawo ma Makarantar dauki ganin yanda kokarin da Marigayi Danbaba Suntai ya kawo wannan cigaba a fannin kiwon lafiya, Makarantar da ta kama hanyar durkushewa gadan- gadan saboda halin ko in-kula da Gwamnatin, Gwamna Darius Ishiaku ke nunawa a wannan fannin.

Wasu daga cikin Malaman da suka gabatarwa ‘Jaridar Yan’ ci da hotunan wasu daga cikin Gine-ginen Makarantar na cikin mummunan yanayi sakamakon lalacewa da shudewa baki daya a doron Kasa. Lalatattun Gine-ginen sun hada da Babban dakin bincike da gwaje-gwajen sinadarai, Gidajen Ma’aikata, Dakunan Karatu da sauran Ofisoshin ayyukan gudanarwan Makarantan. Wani abun takaici anan shine, wannan Makarata ce wanda ake koyar da Dalibai aikin kiwon lafiya, wanda hakan ko kadan baizo dai-dai da tanadin Dokan karantarwa a wannan fannin ba.

“Wannan halin ko in kula da Gwamnatin Taraba ke nunawa wannan fannin bai dace ba, an barmu a baya matuka.

“Rashin Dakunan koyar da karatu masu kyau da sauran kayayyakin aikin gudanarwa ya hana Hukamar da abin yashafa amincemana karantar da wasu Kwasa-Kwasai a Makarantar, wanda ko shakka babu duk Gwamnatin data san abinda takeyi zata dakile wannan matsalar cikin gaggawa, ba zata bari burin Marigayi Suntai akan harkan lafiyan yan Jihar ya shudeba.

“Zun-zurutun Kudi Naira Biliyon Goma sha biyu da digo biyu (11.02bn) aka ware ma harkan Ilimi a Kasafin Kudin shekara na 2020, bayada wasu sauran kasafin Kudin da Gwamna Darius Ishiaku ke gabatarwa Majalisar Jihar, fannin Ilimi ne ke samun kaso mafi tsoka a koda yaushe, amma abun takaici babu wani abun azo a gani a wannan Makarantan.

Inda bincike ya nuna mana cewa bayada Makarantar koyar da Jinya da Anguwan Zoma, Makarantun Sakandare da Makarantun Firamare na fama da irin wannan matsaloli suma, kama daga nan Jalingo Fadan Jiha, da dukkanin sauran Kananan Hukumomin 16 dake fadin Jihar.

Daga bisani, mun tuntubi Kwamishinan Manyan Makarantun Jihar Taraba, Hon. Edward Baraya kan lamarin, sai yace ba’a bashi izinin yin magana da wani kafar yada labarai ba, har sai ya sami izini daga wurin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar ko kuma Sakataren Gwamnatin Jihar kafin yayi magana da manema Labarai.

Labarai Makamanta