Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Lakanin Gyaran Najeriya Na Hannuna – Atiku

Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce Najeriya na bukatar shugabanci wanda zai gyara tattalin arziki da tabbatar da zaman lafiya domin kasar ta dawo cikin hayyacin ta.

Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis 21 ga watan Oktoba a Abuja yayin gabatar da lacca na cika shekaru 70 da kuma gabatar da littafin Shugaban Kamfanin DAAR Communications Plc, Cif Raymond Dokpesi.

Ya kara da cewa kasar na kuma bukatar jagora wanda zai hada kai, sake fasali da tabbatar da tsaron ‘yan kasar.

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019 ya ce shi ne mutumin da ya dace da zai ba kasar abin da take bukata, yana da tabbacin haka sakamakon gogewa da kwarewar shi akan sha’anin Mulki.

“Na fadi hakan a baya, kuma zan maimaita a yanzu cewar “Najeriya na bukatar shugabanci wanda zai iya hada kan kasar, ya kawo kwanciyar hankali, sake fasali da sake fasalin tattalin arzikin da zai kawo tsaro.”

Exit mobile version