Laifin Gwamnonin Yarbawa Ne Kisan Da Ake Yi Wa ‘Yan Arewa A Kudu – Lawan

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ranar Asabar ya soki lamirin gwamnonin Yarbawa dake sashin kudu maso yamma, inda ya ɗaura musu alhakin kashe-kashen da akayi wa al’ummar Arewa da ya faru a kasuwar Shasha a Ibadan, jihar Oyo.

A cewar Lawan, gwamnonin ne suka tunzura matasan yankin wajen kaiwa yan Arewa hari. A hirar da yayi da sashin Hausa na BBC Hausa, Lawan ya ce kiran da wasu gwamnonin kudu maso yamma keyi na korar Fulani daga yankin ya haifar da hakan.

Shugaban Majalisar ya ƙara da cewar ko shakka babu kalaman gwamnonin ne ya haddasa hare-haren da ake kaiwa yan Arewa a kudancin Najeriya. “Abinda ya faru a jihar Oyo, da kuma abubuwan da suka faru a wasu jihohin kudu maso yammacin Najeriya, watakila da kudu maso gabashi, an samu matsalan daga gwamnonin ne.

“Gwamnonin suke ke da hakki muhimmi don kare mutanen dake yankinsu.” “Kuma irin kalamai da wasu gwamnoni sukayi, musamman daga wannan yankin ya taimaka wajen tunzura mutanen yan asalin jihohin, wadanda ke ganin ai shugabanninsu sun basu lasisi ne.”

Idan jama’a basu manta ba a ranar 18 ga Fabrairu, rikici ya barke a Shasha sakamakon rashin fahimta tsakanin wasu kuma yayi sanadiyar rashin rayuka da dukiyoyi, galibi na ‘yan Arewa.

Labarai Makamanta