Labarun Bogi Na Kambama Matsalar Tsaro A Najeriya – Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya ce labaran kanzon kurege na kara ingiza wutar rikici a Najeriya.

Hakazalika labaran sukan kara rura wutar rashin tsaro da yi wa kokarin gwamnati kafar angulu da kuma kara fusata yan kasa, tare da haifar da rashin yarda tsakanin al’umma da gwamnati.

Buhari ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da yake wani taron ilimantarwa na UNESCO game da kafofin yada labarai na duniya wanda zauren matasan Najeriya ke karbar bakunci.

Buhari wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa Ibrahim Gambari ya ce, samun bayanan da za a dogara a kansu kullum shi ne yadda za a samu tsaftatattun bayanai, kuma babu abin da suke yi sai haifar da barazana a cikin al’umma.

Labarai Makamanta