Kyandar Biri: Hukumar Lafiya Ta Kalubalanci ‘Yan Luwadi Su Rage Barbara

Hukumar Lafiya ta Duniya ta shawarci maza da ke neman ‘yan uwansu maza da su rage yawan abokan mu’amular tasu, domin takaita yaduwar cutar kyandar biri.

Ta kuma nemi su dinga musayar bayanai game da su.

Kashi 98 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar maza ne masu neman maza ‘yan uwansu.

WHO ta ce an bayar da rahoton mutum 18,000 a kasashe 78 da suka kamu, galibi a kasashen Turai.

An samu mutuwar mutum biyar.

Shugaban hukumar, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce za a iya dakatar da cutar – idan kasashe, al’ummomi da kuma daidaikun mutane sun bi daukan matakan da suka dace.

Labarai Makamanta