Kyakkyawan Karshe: Ya Rasu Yana Cikin Sujada A Sokoto

Wani Dattijo mai shekaru 71 mai suna Malam Ahmad Abdullahi, wanda aka fi sani da Asi, ya mutu a yayin da ake sallar Juma’a, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Malam Ahmad ya rasu ne a Masallacin Sultan Bello, dake Sokoto a yayin da yake gabatar da raka’o’i biyu na sallar Juma’a.

A cewar wasu masallata, ya mutu ne a lokacin da ake gabatar da raka’ar karshe, inda ya kasa dagowa daga sujjada.

Babu ciwo babu komai a tare da wannan bawan Allah, an bayyanashi a matsayin mai tsoron Allah, mai ibada, saukin kai da kuma girmama mutane. Yayi suna matuka a yankinsu saboda halayenshi na kirki.

A safiyar ranar Juma’ar kafin rasuwar tashi, Malam Ahmad ya kaiwa ‘yan uwanshi ziyara a yankin Filin Magaji dake Gidadawa.

Haka kuma wani makocinsa, ya sanar da Daily Trust cewa a wannan ranar, da misalin karfe 9 na safe, yaje wani shago ya siyo reza don tsaftace kanshi a wannan rana mai albarka.

“A lokacin da yake shirin barin shagon sai wani abokinshi da suka saba wasa dashi yake tsonakarshi akan yadda yake riga shi zuwa Masallaci a kowacce rana. Sai ya c mishi yau ma zan riga ka zuwa In Sha Allah,” cewar makocin nasa.

Matarshi Malama Halima, wacce ke da shekaru 58 kuma ta aureshi kimanin shekaru 34 da suka wuce, ta ce mijinta mutumin kirkine babu ruwan shi, kuma sun haifi yara uku tare Saudatu, Zahra’u da kuma Abubakar.

“Ya tafi masallacin tare da ‘yan jikokinmu, wannan ne karshen ganina da shi,” cewar Halima.

Da take ba da labarin yadda ta sami labarin mutuwar mijinta, ta ce, “jim kaɗan bayan sallar Juma’a, na ji hayaniyar mutane a kusa suna fama da wani abu mai nauyi. Sun nemi na shiga cikin daki in ba su wuri.”

Ta ce taki yadda ta shiga dakin saboda duk tabi hankalinta ya tashi ta fara tunanin wani abu.

“Ina tsaye a wajen. Mutane sun shigo tare da gawarsa suka fara rokona in bar komai zuwa ga Allah. Suka ce nufin Allah ne yasa yayi irin wannan mutuwa. Na fadi nan da nan. ”

Da aka tambaye ta ko ta samu wani gargadi game da mutuwar mijinta, Halima ta ce ta fara jin rashin lafiya da kuma rashin nutsuwa a safiyar ranar.

Ta ce mijinta na marigayi koyaushe yana cikin addu’o’i da rokon Allah bukatunsa; kuma yana kaunar yara.

Malama Halima ta tuna shekarun da suka kwashe tare: “A shekaru 34 da muka kwashe tare, bamu taba yin rikici ba, ko daidai da rana guda.

Related posts