Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Kwastam Ta Kama Fetur Na Miliyoyi Ana Yunkurin Fitarwa Waje

Hukumar Kwastam da ke yaƙi da fasa kwabri ta ƙasa ta ce ta kama man fetur da ya kai kimanin lita 81,425 da ake shirin fita da shi daga ƙasar.

Hukumar ta ce ta kama man fetur ɗin a Badagry da ke Legas da kuma kan iyakar Najeriya da Jamhuriyyar Benin.

A wani saƙo da hukumar ta kwastam ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce an ɗura man fetur ɗin cikin duro-duro kusan 60 sa’annan aka saka wani man a cikin buhuna da ku ma jarkoki.

Hukumar ta ce darajar man fetur ɗin da jami’anta suka kama ya kai sama naira miliyan 13.

Exit mobile version