Kwara: Matasa Sun Yi Zazzafar Zanga-zanga Saboda Tsadar Wiwi

Matasa a Birnin Ilori na jihar Kwara sun fita zanga-zanga inda suka rika lalata kayan mutane wai duk saboda tabar wiwi da ake sayar musu ta kara kudi.

Saidai kuma Rahotanni sun bayyana cewa hakarsu ta cimma ruwa saboda bayan wannan tada hankali da suka yi, farashin tabar wiwin ya sauko kasa, kamar yanda jaridar Guardian ta ruwaito.

Saidai wannan lamari ya tadawa mutanen garin hankali, musamman ma shuwagabannin addinai, babban limamin Ilori, Alhaji Muhammad Bashir ya bayyana cewa garin ba haka yake ba a shekarun baya, matasan suna daukar muguwar dabi’a ne daga mutanen banza, ya kara da cewa sai iyaye sun dage da baiwa ‘ya’yansu tarbiyyar data kamata.

Shima shugaban kungiyar CAN na jihar, Dr. Olusola Ajolore ya bayyana cewa ya kamata a dauki mataki da gaggawa akan wannan lamari inda yace matasa ne kashin bayan al’umma.Idan akayi sakaci da lamarin matasa za a samu matsala mai yawa nan gaba

Labarai Makamanta