Kwankwaso Zaman Dumama Kujera Ya Yi A Majalisa – Shekarau

A ranar 21 ga watan Yulin 2021 ne a wata ziyarar barka da sallah da kwamitin Shura suka kaiwa Sanatan Kano ta Tsakiya Mallam Dakta Ibrahim Shekarau da a jawabin sa ya ce wakilcin da muka yi kowa ya gani ko yana ji a Rediyo da Soshiyal Midiya na ayyukan da muka ɗan jajjefa a mazaɓu da ƙananan hukumomi da sunan aikin Constituency Project, duk ana kan wannan a yi ta haƙuri a ƙananan hukumomin da ba mu samu mun taɓa ba a cikin 15 ɗin nan a na nan tafe ana ɗan jefawa, kuma ba tare da mun zargi kowa ba wasu na cewa ayyukan da ake yi ba mu yi ba.

Mallam ya ƙara da cewar amma shekaru 4 kan ya zo su dai basu ga komai ba ga wanda suka gada, Ya ce wannan ya rage na ƴan Kano Ta Tsakiya su tambayi tsohon Sanata abokin sa aminin sa cewa shin kason nan da ake bayarwa ga kowane ɗan majalissa na ayyukan mazaɓu ina na’sa na shekara 4 ina aka kai su? Masu tambaya su tambayo ƴan Kano Ta Tsakiya ba magana ce ta jam’iyya ba, domin da wanda ya zaɓe ka da wanda bai zaɓe ka ba wakilci naka ne.

Mallam ya ƙara nanata cewar mu ƴan Kano Ta Tsakiya da aka wakilce mu shekara 4 daga shekara ta 2015 zuwa 2019 ina ayyukan mu na Constituency Project? na shekara 4 mu dai ba mu ji ba kuma ba mu gani ba, amma muna kyautata zaton an yi ji ne ba mu yi ba. Amma dan ku gamsu wataƙila ko shi ko na kusa da shi su tallata mu ji dan muna da haƙƙi dimokuraɗiyya shi ne wanda yake shugabanci ya faɗa dan jama’a su sani wanda ake shugabanta su tallata da a sani – Inji Mallam Ibrahim Shekarau.

Ba mu ce mun fi kowa ba, ba mu ce yaadda muke yi ba za a yi ba fatan mu shi ne wanda suke yi mana wakilci daga ƙananan hukumomi da majalissun jiha da na tarayya da na dattawa, Ana bayar da irin wannan Constituency Project ɗin kuma za mu so mu ji da ina da ina ake yi.

Labarai Makamanta