Kwankwaso Ya Karyata Jita-Jitar Komawa APC

Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana a game da rade-radin da ake yi na cewa yana shirin barin PDP.

Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa har gobe yana nan a jam’iyyar PDP, babu wata magana mai kama da zai koma APC sai dai shaci fadi na mutane kawai. Kwankwaso ya yi wannan bayanin ne a hirar da akayi dashi a gidan talabijin na Arise.

Shugaban siyasar Kwankwasiyyan ya yi wannan martani ne yayin da aka jefa masa tambaya kai-tsaye da ake hira da shi a game da makomarsa, da kuma rade radin da ake yi na cewar zai sauya sheka zuwa APC.

Tsohon Gwamnan yace zai yi zamansa a jam’iyyar hamayya ta PDP, ya hada-kai da sauran abokan aikinsa wajen ganin an shawo kan rikicin cikin gida dake addabar Jam’iyyar.

Labarai Makamanta