Kwankwaso Ya Bada Tallafi Ga ‘Yan Arewa Da Rikicin Oyo Ya Shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bada gudunmuwan kayan abinci ga jama’ar Arewan waɗanda rikicin Shasha a jihar Oyo ya shafa, domin rage musu raɗaɗi.

Tsohon shugaban karamar hukumar Tarauni, Muktar Umar Yarima, ya jagorancin tawagar Kwankwasiyya zuwa Oyo ranar Juma’a domin gabatar da gudunmuwar ga shugabannin Hausawa dake jihar a madadin Sanatan.

Kayan abincin sun hada da buhun shinkafa 200, katon 200 na ruwan gora, da kuma lemun kwalba katon 200 da sauran wasu kayayyakin.

Yayin gabatar da kayan, Yarima yace, “Jagoranmu ya samu labarin cewa mutanen nan sun rasa muhallinsu kuma suna cikin halin kunci kuma suna bukatan taimako.” “Shi yasa jagoranmu ya bada gudunmuwar wadannan kayan abincin domin raba musu.”

Yarima ya yi kira ga sauran shugabannin su taimakawa mutanen da suka rasa muhallansu duba da irin mawuyacin halin da suka shiga.

Labarai Makamanta